Saurari Sharhi Radio

Katafariyar Matatar Ɗanyen Mai ta Ɗangote Rifirenery, ta fara sayar da tataccen fetur ga ‘yan kasuwar cikin gida a ranar Talata. Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa an fara sayar da fetur ɗin ne a ranar Talata, tare da ruwaito bayanin daga bakin Babban Daraktan matatar, Devekumar Edwin.

Wannan gagarimar nasara dai wasu dillalan fetur na cikin gida sun tabbatar da hakan su ma, kamar yadda ƙungiyar masu sayar da fetur a Najeriya suka bayyana.

“Mu na da wadataccen fetur a ƙasa. Ana ci gaba da lodi da jigilar fetur zuwa wurare daban-daban ta ruwa da kuma ta kan titina.

“Jiragen ruwa ga su nan birjik sun yi layi, ana ci gaba da loda masu fetur ɗaya bayan ɗaya. Banda fetur kuma ana lodin man da jiragen sama ke amfani da su.

“Jiragen ruwa sun yi lodin lita miliyan 26, amma dai muna ƙoƙarin mu ga mun samu jiragen da zasu iya kwashe lita miliyan 37, domin sauƙaƙa jigila,” Haka Edwin ya bayyana wa Reuters.

Da ya ke magana kan fara sayar da mai ga ‘yan kasuwar cikin gida, Shugaban IPMAN, Abubakar Maigandi ya ce sun amince za su riƙa sayen za a riƙa sayar masu da man dizal duk lita 1 kan 1,225 ($0.96), bisa yarjejeniyar cewa tunda da yawa za su riƙa saye.

Ya ce mambobin ƙungiyar IPMAN su na da gidajen mai kimanin 150,000 a faɗin ƙasar nan.

Sai dai kuma ƙananan ‘yan kasuwa da masu daffo-daffo na nan na ƙoƙarin samun takardun yarjejeniyar karɓar basussuka daga bankuna, domin su fara sayen mai daga Matatar Ɗangote.

Matatar Ɗangote ta fara tace dizal da man jiragen sama tun a cikin Janairu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *