Saurari Sharhi Radio

Takaddama ta barke a kasar Ghana bayan da wani malamin addinin gargajiya dan shekaru 63 ya auri wata matashiya mai shekaru 13, inda mutane da dama ke kira ga mahukunta da su kama shi.

 

Malamin addinin gargajiyar mai suna Nuumo Borketey Laweh wanda aka fi sani da Gborbu Wulomo ya auri yarinyar ne a gagarumin bikin da aka gudanar a wani karamin kauye dake wajen birnin Accra.

Tuni dai ‘yan sanda suka buda bincike kan wannan aure, yayin da jami’an tsaro suka killace yarinyar da mahaifiyarta don basu kariya, a cewa Ofishin Antoni Janar na kasar.

Bayanai na cewa idan har zargin da ake yi ya tabbata kan tsohon, zai fuskanci tuhumar cin zarafin kananan yara wanda hakan kuma ya ci karo da dokokin kasar, da ya kayyade shekaru 18 a matsayin shekarun aure.

 

Sai dai da yake kare kansa ta bakin mai magana da yawun sa, malamin addinin gargajiyar ya ce ba wai an kulla auren da yarinyar ne don ta sauke nauyin aurenta a yanzu ba, a’a za’a bata dama har sai ta kai shekaru 18 tukunna.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *