Saurari Sharhi Radio

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce yankuna 551 a sassan ƙananan hukumomi 12 ne hare-haren ƴan bindiga suka shafa lamarin da ya ɗaiɗaita mutum 289,375.

Dakta Usman Hayatu Mazadu, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar ne ya bayyana haka lokacin rarraba kayan taallafi a Maraban Kajuru

Ya ce a yankin Chikun, yankuna 134 lamarin ya shafa sannan mutum 26,345 ne suka rasa gidajensu.

“A Birnin Gwari, hare-haren sun shafi yankuna 84 sai 70,893 da suka ɗaiɗaita.” kamar yadda jami’in ya bayyana.

Dakta Mazadu ya jaddada buƙatar a samar wa mutanen da lamarin ya shafa tallafi inda ya bayyana mummunan tasirin da hare-haren suka yi wa yankunan.

Bbc Hausa ta ruwaito cewa Kaduna na cikin jihohin da suke fama da matsalar ƴan bindiga masu satar mutane don kuɗin fansa inda ko a baya-bayan nan an sace gomman ɗalibai tare da malaminsu a yankin Kuriga.

Sai dai jami’an tsaro sun kuɓutar da su bayan kwanaki a hannun ƴan bindigar da suka yi awon gaba da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *