Saurari Sharhi Radio

Martanin shugabannin Iran kan harin
Harin dai ya janyo suka daga manyan jami’an Iran da kuma barazanar mayar da martani a kan Isra’ila.

“Za mu mayar musu da martani ta yadda sai sun yi da-na-sanin abin da suka aikata”. In ji jagoran addinin Iran Ali Khamenei.

Shi kuwa shugaba Ebrahim Raisi, kiran harin ya yi a matsayin rashin imani da tausayi wanda kuma ba za a amince da shi ba.

Cikin wata tattaunawa da suka yi ta waya tare da takwaransa na Syria, ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya bayyana harin a matsayin abin da ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Ya nuna wa Isra’ila yatsa, inda ministan harkokin wajen Iran din Amir-Abdollahian ya ce firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya samu ‘matsala a kwakwalwarsa’.

Ra’ayoyin masana kan martanin Iran
Wadannan kalamai sun sanya fargabar karuwar zaman dar-dar a tsakanin Isra’ila da Iran, to amma kwararru sun shaida wa BBC cewa, martanin da Iran din za ta mayar ba lallai ya yi tasiri ba.

“Iran ba ta da karfin da za ta tunkari Isra’ila bisa la’akari da karfin sojinta da yanayin siyasa da tattalin arzikinta.” in ji Ali Sadrzadeh, mai sharihi a kan al’amuran da suka shafi Gabas ta tsakiya.

“To amma ya kamata su yi wani abu wanda a nan gaba ba za a kara kai musu irin wannan hari ba, ko kuma su yi abin da za su kare kansu.”

Wannan dai ra’ayin Fawas Gerges ne, wanda ya yi amanna cewa Iran ba za ta iya yi wa Isra’ila komai ba, duk da Isra’ilar ta yi matukar cin mutuncinta.

Gerges ya ce mai yiwuwa Iran ta hakura, saboda ta gwammace fifita manufarta guda ta hada makamin nukiliya.

“Iran na kara samun karfin iko, tana da makamashin uranium, tana samun nasara a wa su abubuwanta.

Yanzu abin da ya kamata Iran ta yi shi ne ba wai ta aike da makamai masu linzami 50 don ta kashe Isra’ilawa 100 ba ne, ta tabbatar ta tsare gidanta ba kawai daga hare-haren Isra’ial ba har ma na Amurka”. In ji Gesges.

Tun bayan fara yakin Isra’ila a Gaza, hare-haren makamai masu linzami da na jirage maras matuka da mayakan Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran a Syria da Iraqi da Lebanon da kuma Yemen ke kai wa a kan Isra’ila ke kara karuwa, to amma kamar sun takaita ayyukansu na takalar Isra’ilan.

To ko akwai yiwuwar ‘yan Hezbollah wadanda suka saba musayar wuta da Isra’ila za su mayar da martani a kan harin Damascus?

Ko Iran za ta yi amfani da Hezbollah?
Hezbollah na daya daga cikin kungiyoyin da ke da manyan makamai da kuma mambobi, wani kiyasi da aka yi ya nuna cewa kungiyar na da mambobi tsakani dubu 20 da dubu 50, kuma yawancinsu sun samu horo sosai.

Bugu da kari, kungiyar na da akalla makaman roka dubu 130 da masu linzami da dama.

Kwararrun da BBC ta tattauna da su sun ce ba lallai ba ne kungiyar ta kaddamar da wani babban hari kan Isra’ila ba.

“Hezbollah ba ta son ta fada tarkon Isra’ila saboda ta fahimci cewa Benjamin Netanyahu da kuma ‘yan majalisar na duba yiwuwar fadada yaki da suke.

Makomar siyasar Benjamin Netanyahu ta dogara ne a kan ci gaba da yakin da ake a Gaza sannan yakin na karuwa a arewacin Gaza inda ake gwabzawa da ‘yan Hezbollah da kuma Iran din kanta.” in ji Fawaz Gerges.

Ali Sadrzadeh, ya yi amanna cewa akwai yiwuwar Iran ta dan mayar da martani mai makon ta shiga yaki da Isra’ila.

“Iran ta kware wajen kai manyan hare-hare kamar irin wanda ta kai a matsayin martani bayan da aka kashe mata babban kwamandanta, Qasem Soleimani.” in ji Sadrzadeh, yana mai bayar da misali da harin makami mai linzamin da Iran ta kai wa sansanin Al Asad a Iraq a ranar 8 ga watan Janairun 2020.

Iran ta kai hari sansanin Al Asad domin mayar da martani a kan wani hari da Amurka ta kai da jirgi maras matuki Bagadaza da ya yi sanadin mutuwar babban kwamandanta Qasem Soleimani.

BBC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *