Saurari Sharhi Radio

Kotun da’ar ma’aikata (CCT) a ranar Alhamis ta dakatar da Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano.

A ranar Alhamis ne aka gurfanar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a gaban kuliya bisa zargin saba ka’idojin da’ar ma’aikata da cin hanci da rashawa, cin zarafin mukami, bayyana kadarorin karya, da karbar kyaututtuka da dai sauki.

Kotun ta amince da bukatar mai shigar da kara inda ta umurci wanda ake kara da ya koma gefe a matsayinsa na Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano bisa zargin saba wa tanadin kundin da’ar ma’aikata da kuma Kotun ta CAP C15 LFN 2004 da ke jiran sauraron karar.

Kotun ta umurci Gwamnan jihar Kano da Sakataren Gwamnatin jihar Kano da su dauki dukkan matakan da suka dace don nada jami’in zai karbi mukamin Shugaban riko na Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa har zuwa lokacin da za a saurari Shari’ar tare da yanke hukuncin

Ko da yake, wata majiya a gwamnatin jihar Kano ta shaida wa SOLACEBASE cewa gwamnati za ta daukaka kara kan hukuncin saboda akwai umarnin kotu da ya hana gurfanar da shi, da kuma tsare-tsare na hukumar da’ar ma’aikata da EFCC da sauran su.

Idan dai za a iya tunawa gwamnatin jihar Kano ta maka gwamnatin tarayya a gaban babbar kotun jihar kan abin da ta bayyana a matsayin cin zarafi da kuma tursasa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar (PCACC) da wasu hukumomin tarayya uku ke yi.

Wannan ya biyo bayan gayyatar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da kuma Code of Conduct suka aike wa Hukumar PCACC da jami’anta domin amsa tambayoyi kan yadda Hukumar ta gudanar da mulki tun daga shekarar 2011 zuwa yau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *