May 29, 2023

Ƙwararru A Harkar Kimiyya Da Ke Tattara Asarar Da Wasu Mugayen ƙwari Suka Haifar A Faɗin Duniya Sun Gano Wasu Halittu Biyu Da Suka Jawo Asarar Fiye Da Sauran.Nau'in kwaɗo ɗan Amurka da ake kira American bullfrog a Turance da kuma jan maciji - da ake kira brown tree snake a Turance - sun haddasa asarar kuɗin da suka kai dala biliyan 16 da 300,000 - kwatankwacin naira tiriliyan shida - faɗin duniya tun daga shekarar 1986.

Ƙari a kan albarkatun tsirrai da suka lalata, mugayen dabbobin sun kuma lalata amfanin gona sannan suka haifar da katsewar wutar lantarki.

Masu bincike na fatan abin da suka gano zai taimaka wajen tara kuɗaɗe don daƙile ayyukan mugayen dabbobi a nan gaba.

Cikin rahoton binciken da suka wallafa, masana kimiyya sun ɗora wa jan macijin alhakin haifar da ɓarnar dala biliyan 10.3 jimilla - ta hanyar karaɗe wasu tsibirai a yankin Pacific.

A yankin Guam, inda sojojin Amurka suka ƙaddamar da macijin a ƙarnin da ya gabata, 'ya'yan nau'insa sun haddasa ɗaukewar wutar lantarki da yawa saboda suna maƙalƙalewa kan wayoyin lantarki tare da haddasa asara mai yawan gaske.

Akwai nau'in wannan maciji kusan aƙalla miliyan biyu a ɗan ƙaramin tsibirin, inda wasu alƙaluman ke cewa akwai aƙalla guda 20 a tsawon kowace girman eka na dajin Guam.

Ana ganin dazukan da ke tsibirai sun fi fuskantar hatsarin muggan dabbobi - inda suke yawan saka sauran dabbobin da ke rayuwa a wurin cikin haɗarin ƙarewa a ban-ƙasa.

Mky Kano

mky@sharhi.net

Kamilu

Follow Me:

Comments