May 29, 2023
Labarai

Kuji Wani Aikin Abinkunya Da Amurka Tayi Satar Mai A Kasar Sham

Abokai, kwanan baya an bankado wasu ayarin motocin dakon mai na sojin Amurka sunafitar da man da suka sata daga kasar Sham zuwa sansaninsu dake Iraqi ta wata hanya da ta hada kasar Sham da Iraqi.

Tundaga shekarar 2015, Amurka ta fara aikata irin wannan laifi,awatan Agustan da muke ciki kadai,Amurka ta aikata irin wannan abin kunya na satar mai da fitar da shi zuwa Iraqi har a kalla sau 6.

Yayinda fararen hula a birnin Damascus babban birnin kasar, ke dogoyen layi don sayen man. “Duniya a zanen MINA” na zana wani hoto game da yadda Amurka ta saci mai a kasar Sham.

Hukumar man fetur da albarkatun ma’addinai ta kasar Sham ta ba da sanarwa a kwanan baya cewa, a watanni shida na farkon wannan shekara, a ko wace rana ana samar da man da ya kai ganguna dubu 80.3 a kasar, amma Amurka da dakarunta sun sace kaso 80% daga cikinsu.

Rahotanni na cewa, kasar Sham ta yi asarar kudaden da suka kai kimanin dalar Amurka biliyan 100 sakamakon satar mai da Amurka ta yi.

S M kabara

Mky Kano

mky@sharhi.net

Kamilu

Follow Me:

Comments