March 29, 2024
Wasanni

An Yi Waje Da Juventus Daga Champions League

Juventus ba ta kai zagayen kungiyoyi 16 da za su buga zagayen gaba ba a Champions League, bayan da Benfica ta doke ta 4-3 ranar Talata.

Karon farko da aka fitar da kungiyar Italiya daga wasannin rukuni tun bayan kakar 2013/14.

Kocin Juventus, Massimiliano Allegri ya ce suna bayar da hakuri suna bakin ciki da hakan ta faru, amma bai yadda cewar ya gaza da kungiyar ta kasa kai wa zagaye na biyu ba.

Allegri ya ja ragamar Juventus ta lashe Serie A karo biyar a jere da zuwa wasan karshe karo biyu a Champions League a lokacin da ya fara aiki daga 2014 zuwa 2019.

Da wannan sakamakon Benfica ta bi sawun Paris St Germain zuwa mataki na biyu a babbar gasar tamaula ta Zakarun Turai.

PSG wadda ta casa Maccabi Haifa 7-2 ta ja ragamar rukuni na takwas da maki 11, iri daya da na Benfica ta biyu.

Juventus tana ta uku da maki uku iri daya da na Maccabi ta hudu.

Juventus, wadda ta kai wasan karshe a Champions League a 2015 da kuma a 2017 za ta koma buga Europa League kenan.

Wannan karin koma baya ne daga Juventus a kakar nan, wadda take ta takwas a Serie A da tazarar maki 10 tsakaninta da Napoli mai jan ragama.

Mky Kano

mky@sharhi.net

Kamilu

Follow Me:

Comments