March 28, 2024
Wasanni

Akwai Yuwuwar A Haramtawa Tunisia Halartar Gasar Cin Kofin Duniya - FIFA

Gargadin na zuwa ne bayan kalaman da ministan matasa da wasanni na Tunisia, Kamel Deguiche ya yi, game da yuwuwar rushe ofisoshin gwamnatin tarayya.

Fifa dai na kallon furucin nasa a matsayin wani yunkuri na yin katsalandan a harkokin gudanarwar hukumar kwallon kafa ta kasar, kuma ta bukaci hukumar da ta yi karin haske game da yunkurin tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida da kuma barazanar rusa ofishinta.

Hukumar mai shalkwata a Zurich ta kuma tunatar da cewa kungiyoyin mambobi ya wajaba a kan su gudanar da al'amuransu ba tare da wata mu’amala ta siyasa ba.

Mky Kano

mky@sharhi.net

Kamilu

Follow Me:

Comments