March 28, 2024
Rikici

Kwamitin Sulhu Na MDD, Ya Amince Da Kudurin Tsawaita Wa’adin Aikin Shirin UNSMIL Mai Wanzar Da Zaman Lafiya A Libya,

Kwamitin sulhu na MDD, ya amince da kudurin tsawaita wa’adin aikin shirin UNSMIL mai wanzar da zaman lafiya a Libya, zuwa ranar 31 ga watan Oktoban 2023.
Daukacin mambobin kwamitin 15 ne suka amince da kudurin mai lamba 2656, tare da yin maraba da nadin Abdoulaye Bathily, a matsayin manzon musammam na sakatare janar na majalisar mai kula da batun Libya, kuma shugaban tawagar UNSMIL. Sun kuma bukaci dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki a kasar Libya, su ba manzon na musammam goyon baya yadda ya kamata, wajen gudanar da ayyukansa.
Har ila yau, kudurin ya yi duba ga muradin al’ummar Libya na gudanar da zabe, inda ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da manyan masu ruwa da tsaki, su amince da tsarin da aka yi na gudanar da zabukan nan ba da jimawa ba, domin kafa gwamnatin hadin kan kasa, wadda za ta jagoranci kasar tare da wakiltar baki dayan al’ummarta.
Bugu da kari, kudurin ya nanata cewa, matakan soji ba za su shawo kan matsalolin kasar ba, inda ya bukaci dukkan bangarori su kauracewa rikici da duk wani abu da ka iya kara fargaba da tsananta rikice-rikice da yin tarnaki ga tsarin zabe ko yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta ranar 23 ga watan Oktoban 2020.

Mky Kano

mky@sharhi.net

Kamilu

Follow Me:

Comments