Hare-haren Rasha Sun Jefa Kashi 10 Na Ukraine A Halin Rashin Lantarki- Zelensky

A jawabin kai tsaye da Zelensky ya gabatar ta video ya ce al’ummar kasar miliyan 4 da dubu 500 yanzu haka basu da lantarki a gidajensu saboda barnar da Rasha ta yi a yankunansu.
A cewar shugaban yankunan kasar 10 ne katsewar lantarkin ta shafa inda ya yi kira gas ashen lantarkin kasar da ya yi kokarin tattala lantarkin kasar don ganin al’umma na rayuwa a cikin haske tare da katse lantarkin wuraren da babu mutanen da ke rayuwa a wajen.
Shugaban na Ukraine ya bukaci katse lantarkin shagunan siyayya bayan rufewa da kuma allunan hanya masu amfani da lantarki don samun wadatuwar lantarkin ga sauran sassan kasar.
Zelensky cikin jawabin nasa ya yi kakkausar suka ga matakin Rasha na sauya matsuguni ga wasu al’ummomin Ukraine da ke rayuwa a yankunan da Moscow ta kwace iko da su.
Tashoshin lantarkin Ukraine da ke da nisan kilomita 25 daga birnin Kherson kusan watanni 8 kenan suna karkashin ikon Rasha lamarin da ya sanya fuskantar karancin lantarkin a sassan kasar.
Comments