Labarai
NAJERIYA DA MEXICO SUN KULLA YARJEJENIYAR KASUWANCIN ZOBO

An ruwaito cewa ƙasar ce kan gaba wajen shigar da ganyen zoɓo Mexico kafin su dakatar da kasuwancinsa a 2017.
Dr Vincent Isegbe, babban darkta a hukumar kula da dabbobi da tsirrai a Najeriya (NAQS), shi ne ya saka hannu a madadin Najeriya inda Dr Javier Arriaga ya wakilci Mexico a birnin Mexico City.
“Wannan yarjejeniya za ta ƙarfafa kasuwanci tsakanin Najeriya da Mexico,” a cewar Jakadan Najeriya a Mexico Rafiu Adejare.
Ya ƙara da cewa yanzu haka akwai ‘yan Mexico da ke gudanar da ayyukan noma a Jihar Gombe da ke arewacin Najeriya.
A 2017, hukumar NAQS ta bayyana cewa Najeriya na samun dala miliyan 35 daga kasuwancin zoɓo a faɗin duniya.
Sanata Ibrahim Hadejia sannu da kokari
Saddam Ibrahim ICT manager kaugama
Comments