December 10, 2023
Ilimi

ASUU Ta Shiga Ganawar Sirri Da Mambobinta

Shugabannin Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya ASUU sun shiga ganawar sirri ta gaggawa.

Jaridar Daily Trust Najeriya ta ruwaito cewa kungiyar ta shiga ganawar sirrin ne da tsakar ranar Litinin, a harabar sakatariyar kungiyar da ke jami'ar Abuja.

Ganawar karkashin jagorancin shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke, za ta duba batun biyan malaman rabin albashin watan Oktoba.


Mky Kano

mky@sharhi.net

Kamilu

Follow Me:

Comments