Labarai
Ayau Ake Makoki Kan Yadda Gobarar Ta Kashe Mutane 21 A Zirin Gaza

An lullube da tutocin Falasdinawa, wadanda suka mutu ta hanyar cincirindon jama'a zuwa makabartar Beit Lahia inda aka binne su. Yayin da har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, mai magana da yawun hukumar tsaron farar hula ta Hamas a Gaza ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an ajiye kayan man fetur a ginin mai hawa uku. “Ba mu san ainihin abin da ya faru ba,” in ji Mahmoud Abu Raya, wani dan uwan wadanda abin ya shafa, yana mai bayanin cewa gobarar ta tashi “a yayin wani taron dangi.
Rahotannin Falasdinawa sun ce akasarin wadanda suka mutun sun fito ne daga iyali guda - mai suna Abu Raya - wadanda suka taru domin murnar dawowar wani dan uwa daga kasashen waje. Tare da karancin wutar lantarki a yankin da ke fama da talauci, ana samun yawaitar gobarar cikin gida, yayin da mutanen Gazan ke neman madadin hanyar dafa abinci da haske, gami da fitulun kananzir. Ministan tsaro mai barin gado Benny Gantz ya nuna juyayi ga "mummunan bala'i" a Gaza. Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, wanda ke da hedkwata a gabar yammacin kogin Jordan - wani yanki na daban na Falasdinu - ya dauki gobarar a matsayin " bala'in kasa," in ji kakakinsa.
Comments