An Sake Buɗe Kan Iyakar Pakistan Da Afganistan Bayan Harbe-harbe Da Ya Yi Sanadiyar Rayuka

Islamabad, Pakistan – An sake bude wata muhimmiyar mashigar kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan kwanaki biyu bayan musayar wuta da aka yi a kan iyakar Pakistan ta kashe akalla fararen hula 9 da wani sojan Afghanistan. Abdul Hameed Zehri, wani jami'i a Chaman kamar yadda aka san mashigar ta bangaren Pakistan, ya fada wa Al Jazeera a ranar Talata cewa lamarin ya dawo daidai.
“Yankin a bude yake don kasuwanci da farar hula kamar yadda aka saba. Al'amura suna tafiya lafiya kuma halin da ake ciki ya kwanta a nan," in ji Zehri. Mashigar kan iyakar Chaman, mai nisan kusan kilomita 120 daga arewa maso yamma da Quetta, babban birnin lardin Balochistan na kudu maso yammacin Pakistan, yana daya daga cikin mashigar da aka fi samun cunkoso tsakanin kasashen biyu kuma dubban mutane ke amfani da su a kowace rana. A ranar Lahadin da ta gabata, sojojin Pakistan sun ce harbe-harbe ba tare da nuna bambanci ba daga bangaren Afghanistan a mashigar, ya kashe fararen hula da dama tare da raunata wasu fiye da goma - tashin hankali na baya-bayan nan a kan iyakarsu.
Washegari, ministan tsaron Pakistan Khawaja Muhammad Asif ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa hukumomin Afghanistan sun ba da hakuri kan harbin.
"Afganistan ce ta fara tsokana. Sojojin mu suna gyaran shingen kan iyaka ne lokacin da dakarun Taliban suka far musu. A zagayen farko na harbin ba a samu asarar rai ba amma a zagaye na biyu sun yi amfani da manyan bindigogi da kuma harsasai wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula.” Inji shi.
Ministan ya kara da cewa jami'an bangarorin biyu sun gana bayan faruwar lamarin, inda hukumomin Afghanistan suka ba da tabbacin ba za a sake samun irin wannan lamari ba. Kabul ya ce akalla sojan Taliban daya ya mutu a harbin ranar Lahadi yayin da wasu 10 suka jikkata.
A cikin wani sakon Twitter a ranar Litinin, Abdul Qahar Balkhi, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Afghanistan, ya ce maimaita irin wadannan abubuwan zai zama abin nadama.
Ya ce gwamnatin Afganistan "a nata bangaren ta dauki tsauraran matakan kariya sannan kuma ta yi kira ga gwamnatin Pakistan da ta mai da hankali sosai wajen hana tada hankali da ke haifar da tashin hankali da kuma yin illa ga dangantaka tsakanin kasashen".
Comments