Rasha Ta Sha Alwashin Lalata Tankar Yakin Da Jamus Za Ta Baiwa Ukraine

Kakakin fadar ta Kremlin, Dmitry Peskov ya ce a hankalce wannan batu ne da sam bai kamata ba, kuma tamkar kasashen da kansu sun kara tsaurarawa Sojin Ukraine domin kuwa za su tsananta kai hare-hare har sai sun kone makaman.
A cewarsa za su kone tankokin kamar yadda suka kone wadanda suka gabace su, duk da kasancewarsu masu matukar tsada.
Rasha ta jima ta na sukar matakin bayar da tankokin yakin na zamani kirar Leopard 2 wanda ta ce ko shakka babu matakin zai wargaza dadaddiyar alaka tsakanin Moscow da Berlin.
Tuni dai kasashen yammaci suka yabawa Jamus wadda a baya ta yi tirjiya kan baiwa Ukraine izinin amfani da nau'in tankar yakin gabanin kada kuri'a kan matakin a zauren Majalisa.
Comments