March 03, 2024
Labarai

Kasar Senegal Ta Kame Hodar Iblis Fiye Da Kilogiram 800 A Kan Ruwa

Sojin ruwan Senegal sun sanar da kwace hodar Iblis mai nauyin kilogiram 805 yayin wani sumame akan ruwa cikin makon da ya gabata

jirgin dauke da hodar iblis din basu bayar da cikakken bayani kan mutanen da ke cikin jirgin ko kuma inda suka nufa ba.

Ko a watan Oktoban da ya gabata sai da hukumar kwastam ta kasar ta kame kilogiram 300 na hodar Iblis da darajar kudinsa ya kai yuro miliyan 37 makare a wata tanka da ta fito daga Mali.

Tsawon shekaru kenan yankin tsakiya da yammacin Afrika na ci gaba da kasancewa mashigar kwayoyi wadanda ake safararsu daga Latin Amurka.

  Wani rahoto da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da safarar miyagun kwayoyi UNODC ya fitar a bara ya bayyana yadda yankin a zama matattarar miyagun kwayoyi.
Mky Kano

mky@sharhi.net

Kamilu

Follow Me:

Comments