October 05, 2023
Labarai

Shin Sake Sabbin Kudi Zai Zama Mafita

Shin Sake Sabbin Kudi Zai Zama Mafita a nigeria

Wannan sauyin kudin a Nigeria Ba zai haifarwa Nigeria Da mai ido ba hasali ma zai dada saka mutane mussamman wanda suke a karkara wahi mawuyacin hali.

Duba da yadda mafiya yawan mutane basu saba da kai kudaden su Banki, bama su gama yarda da bankin ba hakan zai saka su rasa inda zasu tsoma kansu.

Daga lokacin da aka saka wannan doka ta mayar da kudade banki an budawa marsa gaskiya hanyoyi da dama na cutar alumma.

An samar da wani tushe na cin hanci da rashwa a dalilin wannan doka.

A nazarin da mukayi da binciken da muka gabatar mun gano cewar tabbas  wasu suna kwana da yinwa sakamakon wannan sabon tsari da aka shigo da shi wanda a turance ake kira da Digital Currency.
Yana da kyau hukuma ta tsaya ta duba wannan alamari domin kuwa ba karamar cutarwa ba ce ga alummar kasa baki daya.

BY:ISHAQ ABUBAKAR TOFA

Mky Kano

mky@sharhi.net

Kamilu

Follow Me:

Comments