December 10, 2023
Labarai

Cire Sassan Jiki: Ƴansanda Sun Cafke ƙarin Wasu Likitocin Bogi A Plateau

Rundunar yansanda a jihar Plateau a yau Talata ta ce ta kama wasu likitoci biyu da ake kyautata zaton na da alaka da Noah Kekere, wanda ke hannun ƴansanda bisa zargin satar sassan jiki a jihar.

A tuna cewa an kama Kekere ne a makon da ya gabata, biyo bayan korafin da wata mai suna Kehinde Kamal, ta yi, inda ta zarge shi da cire mata kodar guda daya a wani aiki da ya yi mata a 2018.


Bayan kama Kekere, wani dattijo mai shekaru 75 da haihuwa, wanda ya bayyana sunan sa da Ibrahim O. Ejibade, ya fito yana ikirarin cewa likitan ya cire kodarsa daya a farkon wannan shekara.

Da ya ke tabbatar da kama likitocin da ba a bayyana sunayensu ba, kakakin rundunar ƴansanda, Alfred Alabo, ya ce likitocin na bogi na hannun su tare da Kekere.

Alabo ya bayyana cewa kwamishinan ƴansanda zai kafa wani kwamiti mai karfi na kwararrun likitoci don yin bincike sosai kan lamarin.

Ya ce: “Mun samu karin wasu mutum biyu da ake zargi likitocin da a zahiri suka yi wa matar tiyatar. Sun ce suna gudanar da aikin tiyatar da ke da alaka da appendix.

“Mun gayyaci kwararru daga ma’aikatar lafiya ta jihar Plateau, da kuma kungiyar likitocin Najeriya (NMA), domin su ba mu shawarwari da za su taimaka mana.

“Kwamishanan ƴansanda, CP Okoro Julius ya kafa wani kwamiti na kwararrun likitoci don duba wadannan zarge-zargen,” in ji Mista Alabo.   

Mky Kano

mky@sharhi.net

Kamilu

Follow Me:

Comments