Latest News

Cire Sassan Jiki: Ƴansanda Sun Cafke ƙarin Wasu Likitocin Bogi A Plateau

Rundunar yansanda a jihar Plateau a yau Talata ta ce ta kama wasu likitoci biyu da ake kyautata zaton na da alaka da Noah Kekere, wanda ke hannun ƴansanda bisa zargin satar sassan jiki a jihar. A tuna cewa an kama Kekere ne a makon da ya gabata, biyo bayan korafin da wata mai suna Kehinde Kamal, ta yi, inda ta zarge shi da cire mata kodar guda daya a wani aiki da ya yi mata a 2018.

Shin Sake Sabbin Kudi Zai Zama Mafita

Shin Sake Sabbin Kudi Zai Zama Mafita Wannan sauyin kudin a Nigeria Ba zai haifarwa Nigeria Da mai ido ba hasali ma zai dada saka mutane mussamman wanda suke a karkara wahi mawuyacin hali.

Kasar Senegal Ta Kame Hodar Iblis Fiye Da Kilogiram 800 A Kan Ruwa

Sojin ruwan Senegal sun sanar da kwace hodar Iblis mai nauyin kilogiram 805 yayin wani sumame akan ruwa cikin makon da ya gabata jirgin dauke da hodar iblis din basu bayar da cikakken bayani kan mutanen da ke cikin jirgin ko kuma inda suka nufa ba.

Rasha Ta Sha Alwashin Lalata Tankar Yakin Da Jamus Za Ta Baiwa Ukraine

Fadar gwamnatin Rasha ta sha alwashin cewa matukar kasashen yammaci suka ci gaba da aikewa da tankokin yaki Ukraine ko shakka babu Moscow ba za ta gajiya wajen lalata su ba, kalaman da ke zuwa bayan Jamus ta amince da aikewa Kiev tankokin yaki guda 2 samfurin Leopard.

Najeriya Na Fuskantar Kalubale Da Dama; Na Yi Iya Kokarina - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce girman Najeriya da yawan al’ummar kasar ne ke haifar da kalubale da dama da kasar ke fuskanta, amma a fannoni da dama gwamnatinsa na kokari.

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping, Ya Halarci Taron Kolin Kasar Sin Da Kungiyar Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashen Larabawa Dake Yankin Gulf

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron kolin kasar Sin da kungiyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa dake yankin Gulf karo na farko a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar 9 ga wata, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi. Wannan ne dai karo na farko da shugabannin kasar Sin, da shugabannin kasashen mambobin kungiyar suka gana kai tsaye, domin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Ayau Ake Makoki Kan Yadda Gobarar Ta Kashe Mutane 21 A Zirin Gaza

Dubban Falasdinawa ne suka fito a ranar Juma’a don gudanar da jana’izar hadin gwiwa na mutane 21 da suka mutu a wata gobara da ta tashi a wani gini a zirin Gaza. Akalla yara bakwai ne suka mutu a gobarar da ta tashi a sansanin Jabalia a daren Alhamis, in ji shugaban asibitin sansanin, Saleh Abu Lai.