Shin Sake Sabbin Kudi Zai Zama Mafita Wannan sauyin kudin a Nigeria Ba zai haifarwa Nigeria Da mai ido ba hasali ma zai dada saka mutane mussamman wanda suke a karkara wahi mawuyacin hali.
Sojin ruwan Senegal sun sanar da kwace hodar Iblis mai nauyin kilogiram 805 yayin wani sumame akan ruwa cikin makon da ya gabata jirgin dauke da hodar iblis din basu bayar da cikakken bayani kan mutanen da ke cikin jirgin ko kuma inda suka nufa ba.
Fadar gwamnatin Rasha ta sha alwashin cewa matukar kasashen yammaci suka ci gaba da aikewa da tankokin yaki Ukraine ko shakka babu Moscow ba za ta gajiya wajen lalata su ba, kalaman da ke zuwa bayan Jamus ta amince da aikewa Kiev tankokin yaki guda 2 samfurin Leopard.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce girman Najeriya da yawan al’ummar kasar ne ke haifar da kalubale da dama da kasar ke fuskanta, amma a fannoni da dama gwamnatinsa na kokari.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron kolin kasar Sin da kungiyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa dake yankin Gulf karo na farko a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar 9 ga wata, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi. Wannan ne dai karo na farko da shugabannin kasar Sin, da shugabannin kasashen mambobin kungiyar suka gana kai tsaye, domin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakaninsu.
Dubban Falasdinawa ne suka fito a ranar Juma’a don gudanar da jana’izar hadin gwiwa na mutane 21 da suka mutu a wata gobara da ta tashi a wani gini a zirin Gaza. Akalla yara bakwai ne suka mutu a gobarar da ta tashi a sansanin Jabalia a daren Alhamis, in ji shugaban asibitin sansanin, Saleh Abu Lai.
Akalla mata shida ne suka mutu a kasar Poland bayan da likitoci suka ki zubar masu da ciki saboda hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke kan zubar da ciki.