Gwamnatocin kasashen yammacin duniya suna kira ga Rasha da ta janye matakinta na ficewa daga yarjejeniyar hatsi da Majalisar Dinkin Duniya ta kulla, matakin da ke kawo cikas ga kokarin shawo kan matsalar karancin abinci a duniya, yayin da Ukraine ta ce Moscow ta tsara wannan mataki tun da farko. A watan Yuli ne aka sanya hannu kan yarjejeniyar Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya tsakanin Rasha da Ukraine inda Moscow ta ba da damar jiragen ruwan hatsi su bar tashar jiragen ruwa na Bahar Maliya ta Ukraine.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta yi iƙirarin cewa ƙwararrun sojojin ruwa na Burtaniya sun lalata bututun iskar gas a watan da ya gabata, amma Burtaniya ta ce Moscow tana '' ƙirƙira labarai'.
Karancin makamashi matsala ce da galibin kasashen Afirka ke fuskanta, a yayin da kuma nahiyar Afirka ta kasance daya daga cikin sassan duniya da suke karancin karfin tinkarar sauyin yanayi, don haka, ya zama dole kasashen Afirka su bunkasa makamashi mai tsabta a wani kokari na tabbatar da dauwamammen ci gabansu.
Ya ce: "Sun dara 200 suka shigo kauyen cikin dare suka rika zuwa gida-gida suna ikirarin cewa suna neman babur dinsu da aka sace. "Maharan sun yi kokarin soka min wuka a gaban iyalai na kuma na ki fito musu da 'ya'ya na da suka yi ikirarin sun sace musu babura."
Babban Bankin Najeriya ya bayyana cewa ya zubar da biliyoyin daloli na datti da ba a amfani da su a yanzu. Daya daga cikin manyan ayyuka na CBN shine rabon tsaftataccen takardun kudi na Naira. Babban bankin Najeriya CBN zai sake yin amfani da kudin N200 zuwa N1,000 daga 'yan Najeriya
Gwamnatin mulkin Sojin Mali ta mayar da ‘yan sandan kasar karkashin rundunar sojojinta, a kokarin da take yi na murkushe ‘yan ‘ta’adda masu ikirarin Jihadi, wadanda suka shafe shekaru akalla 10 suna addabar sassan kasar.
’Yan majalissar dokokin kasar Iraqi, sun amince da sunayen mutanen da sabon firaministan kasar Mohammed Shia' al-Sudani ya gabatar musu, domin nada su mukaman ministoci.