Latest News

Tashin Hankalin Burkina Faso Ya Raba Mutane Da Gidajensu

Bayanai daga Togo na cewa hare-haren ta’addanci a makwafciyar kasar Burkina Faso ya yi sanadin raba mutane fiye da dubu 4 da muhallan su. Jamhuriyar Benin da Ghana da kuma Ivory Coast na fuskantar baranazar fantsamar hare-haren ta’addanci.

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) Ta Shirya Gudanar Da Tattaunawar Zaman Lafiya Kai Tsaye

Kungiyar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya cewa, matakin wani bangare ne na shirin agazawa sassan dake rikici da juna a arewacin Habasha, don ganin an laluba mafitar siyasa ga rikicin dake faruwa a yankin Tigray na kasar Habasha.

Gwamnatin Ethiopia Da Sojojin Tigrai Zasu Gana Don Tattaunawar Zaman Lafiya Na Farko

Tawagar gwamnatin Habasha da dakarun Tigray da ke hamayya da juna za su gana a Afirka ta Kudu a karon farko a tattaunawar zaman lafiya a hukumance tun bayan barkewar yaki shekaru biyu da suka gabata. Sanarwar da gwamnatin Habasha ta fitar ta ce "Gwamnatin Habasha na kallon tattaunawar a matsayin wata dama ta warware rikicin cikin lumana da kuma karfafa ingantuwar al'amura a kasa". Tawagar gwamnatin Habasha da dakarun Tigray da ke hamayya da juna za su gana a Afirka ta Kudu a karon farko a tattaunawar zaman lafiya a hukumance tun bayan barkewar yaki shekaru biyu da suka gabata.

Sun Kutsa Masallacin Elram Ne Dauke Da Bindigogi Kirar AK47

A cewar kwamandan rundunar ’yan sandan reshen arewa maso gabashin kasar George Seda, rukunin farko na ’yan bindigar su kimanin mutum 5, sun kutsa masallacin Elram ne dauke da bindigogi kirar AK47, inda suka shaidawa masu halartar sallah a lokacin cewa, suna yaki ne da wadanda ba musulmi ba, don haka suna kiransu da su shiga ayyukan kungiyar.

Yakin Ukraine: Rasha Ta Kai Manyan Hare-hare Kan Tashar Makamashi - Zelensky

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa, kasar Rasha ta kaddamar da wani sabon kazamin hari a kan tashar makamashin Ukraine. Ya ce hare-haren sun yi nisa sosai, inda suka afkawa yankunan Ukraine a yamma, tsakiya, kudu da gabashi.

Iran Ta Bude Karamin Ofishin Jakadanci A Kapan Na Kasar Armeniya Yayin Da Take Fadada Alaka

Iran ta bude karamin ofishin jakadancinta a birnin Kapan na kasar Armeniya a wani abu da ake ganin a matsayin sako kai tsaye ga Azarbaijan da Turkiyya mai goyon bayanta.

Falasdinawa A Gaza Sun Yi Zanga-zangar Nuna Adawa Da Tashin Hankalin Da Isra'ila Ke Yi

Masu zanga-zangar sun rike tutoci domin nuna goyon baya ga wadanda rikicin Isra'ila ya shafa a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye da kuma gabashin birnin Kudus.