Latest News

DA ƊUMI-ƊUMI: Ofishin Yakin Neman Zaben PDP Na Gombe Na Ci Da Wuta

A yanzu haka ofishin yakin neman zaben Mohammed Barde, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Gombe ya na nan na cin da wuta. Daily Trust ta rawaito cewa ana zargin wasu ƴan bangar siyasa ne su ka kona ofishin da ke kusa da masaukin shugaban kasa na gidan gwamnatin Gombe a safiyar yau Litinin.

Za A Gudanar Da Taron Baje Kolin Sararin Samaniya Na Kasa Da Kasa Karo Na 14

Za a gudanar da taron baje kolin sararin samaniya na kasa da kasa karo na 14 a birnin Zhuhai da ke gabashin kasar Sin daga ranar 8 zuwa 13 ga wata. Kwanan baya, manyan jiragen sama masu dakon kaya kirar Y-20 guda 2 sun taimaka wajen yin jigilar kayayyaki zuwa wajen taron. (Tasallah Yuan)

Hare-haren Rasha Sun Jefa Kashi 10 Na Ukraine A Halin Rashin Lantarki- Zelensky

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce kashi 10 cikin 100 na al’ummar kasar yanzu haka na rayuwa ba lantarki sakamakon hare-haren Rasha da suka yi illa ga turakun wutar lantarki.

Darajar Naira Na Kara Faduwa A Kasuwar Canji

Darajar Naira na kara kasa a canjin dala inda hakan ke karfafa fargabar kara tashin farashin muhimman kayan masarufi. Wannan lamari abun lura ya tabbata a karshen makon nan inda dala a canjin hukuma ta haura Naira 444 inda a kasuwar canjin a ke sayen ta kan Naira 778 a kuma sayar kan Naira 783.

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kwace Gidaje Da Motoci Diezani A Abuja.

Mai shari’a Mobolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya, dake Abuja ranar Litinin, 24 ga watan Oktoba, 2022 ta bayar da kayan karbe wasu gidaje biyu a Abuja tare da wasu motocin alfarma na tsohuwar Mai Diezani Alison-Madueke, ga Gwamnatin Taraiyya.

Sama Da Mutane 60 Ne Suka Mutu Sakamakon Ambaliyar Ruwa Da Zaftarewar Kasa A Philippines

Akalla mutane 67 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon zaftarewar kasa da ambaliyar ruwa a kudancin kasar Philippines a ranar Juma'a. Rahotanni daga NDTV sun nuna cewa masu aikin ceto na kokarin ceto mazauna wani kauye mai tsaunuka da aka binne a cikin laka.

Shugaban Nijer Mohammed Bazoum Ya Jagoranci Bikin Rantsar Da Shugaban Kotun Daukaka Kara Na Farko,

Shugaban Nijer Mohammed Bazoum ya jagoranci bikin rantsar da shugaban Kotun daukaka kara na farko, a kasar Abdou Galadima, da na shugaban majalisar jaha na farko, Mista Nouhou Hamani Mounkaila. An gudanar da bikin ne a cibiyar taron kasa da kasa ta Mahatma Gandhi da ke birnin Niamey.