Latest News

Man Fetur: Kamfanin NNPC Ya Rage Farashin ‘yan Kasuwa Domin Saukaka Karancin Man

A jiya ne Kamfanin Mai na Najeriya, NPL, ya dauki wasu sabbin matakai da nufin tabbatar da wadatar mai a fadin kasar nan, ta hanyar kayyade Naira 148 kan kowacce lita a matsayin farashin daga man fetur a gidajen man fetur. Har ila yau, an amince da samar da hajoji masu inganci ga ‘yan kasuwar mai masu zaman kansu, don kawo karshen karancin kayayyakin. Hakan ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan kasuwar masu zaman kansu suka ce suna kwashe kayan ne daga ma’aikatun masu zaman kansu a kan kimanin Naira 200 kan kowace lita, wanda hakan ya sa suka kasa cika umarnin hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, na sa’o’i 48 a makon jiya. Sun kuma bayyana cewa lamarin ya sa sun kasa sayar da man fetur a kan Naira 170 kan kowace lita kamar yadda takwarorinsu na manyan ‘yan kasuwar da kuma kamfanin NNPC.

Rahotanni Sun Ce, Shugaban Amurka, Joe Biden, Ya Ce Zai Matsawa Kasashen Japan Da Holland Lamba

Rahotanni sun ce, shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce zai matsawa kasashen Japan da Holland lamba, don bukatar su hana fasahohin zamani na kera bangarorin hada na’urorin laturoni su shiga kasar Sin.

An Kusa Kammala Aikin Samar Da Wutar Lantarki Na Zungeru

An kusa kammala aikin samar da wutar lantarki na Zungeru, in ji Ministan Lantarki na Najeriya Abubakar D Aliyu. Ministan ya ce a yanzu an kammala fiye da kashi 96 na aikin wanda Idan an kammala zai samar da megawatts 700. 📸 Ma’aikatar Wutar Lantarki a Najeriya

Manyan Kamfanonin Fasahohin Sadarwa Na Amurka Na Yiwuwar Fadawa Matsin Tattalin Arziki

Manyan kamfanonin fasahohin sadarwa na Amurka tun daga Google, da Microsoft da GE, zuwa kamfanin kera kayan wasa na Mattel, sun fara shiga yanayi na koma baya, ko hasashen fuskantar ci bayan ribar da suke samu, yayin da ake nuna damuwa game da yiwuwar fadawa matsin tattalin arziki, da faduwar darajar hannayen jari.

Kamfanin Na Samsung Electronics Ya Sanar Da Cewa Ya Nada Lee Jae-yong A Matsayin Shugaban Zartarwa

Kamfanin na Samsung Electronics ya sanar da cewa ya nada Lee Jae-yong a matsayin shugaban zartarwa, inda a hukumance ya daukaka magajin kamfanin Koriya ta Kudu kasa da watanni 15 bayan da aka sake shi daga gidan yari saboda karbar rashawa.

Gwamnatin Jihar Kogi Da Ke Yankin Tsakiyar Najeriya Ta Shigar Da ƙarar Kamfanin Dangote

Gwamnatin jihar Kogi da ke yankin tsakiyar Najeriya ta shigar da ƙarar kamfanin Dangote kan batun wanda ke da mallakar kamfanin siminti da ke Obajana a jihar.

Ana Ci Gaba Da Yajin Aikin Ma'aikata A Matatun Man Faransa

A Faransa, ana ci gaba da yajin aikin ma'aikata a matatun mai da ma'ajiyar wutar lantarki ta TotalEnergies, yayin da aka sanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a yau Lahadi a birnin Paris bisa kiran 'yan adawar da aka sani da na bangaren hagun.