Latest News

Wani Dan Kasar Libya Da Ake Zargi Da Hada Bam Na Lockerbie A Hannun Amurka Mutumin Da Ake Zargi Da Hada Bam Din Da Ya Kashe Mutane 270 Bayan Ya Tarwatsa Jirgin Pan Am Flight 103 A Shekarar 1988

Wani dan kasar Libya da ake zargi da hada bam din da ya lalata jirgin Pan Am Flight 103 a kan garin Lockerbie na Scotland a shekarar 1988 yana hannun Amurka, a cewar jami’an tsaro a Scotland da Amurka. An shaidawa iyalan wadanda aka kashe a harin bam da ake kira Lockerbie wanda ake zargin "Abu Agela Mas'ud Kheir Al-Marimi yana hannun Amurka", in ji ofishin Crown Crown na Scotland a wata sanarwa a ranar Lahadi.

Yan Sanda Sun Sha Alwashin Bankado Wadanda Suka Kashe Shugaban ADC Na Ogun

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta yi alkawarin bankado wadanda suka kashe shugaban jam’iyyar Ward 15 na African Democratic Congress, Isaga/Ilewo-Orile a karamar hukumar Abeokuta ta Arewa a jihar Ogun, Muhammed Oke.

Turkiya Za Ta Aiko Da Jiragen Sama Masu Saukar Ungulu Zuwa Najeriya

Jakadan Turkiya a Najeriya Hidayet Bayraktar ya ce nan ba da dadewa ba jiragen yaki marasa matuka da jirage masu saukar ungulu daga Turkiyya za su isa Najeriya.

Babu Inda Aka Dasa Bam A Abuja-Yan Sanda

Rundunar yan Sandan Najeriya tace babu gaskiya a cikin labaran da ake yadawa cewar an dasa bama bamai a sassan birnin Abuja a wani yunkuri na kai harin ta’addanci a birnin.

Amurka Ta Umarci Ma'aikatan Difilomasiyyarta Su Fice Daga Abuja

Amurka ta buƙaci wasu daga cikin jami'an diflomasiyyarta da iyalansu su gaggauta ficewa daga Abuja babban birnin Najeriya sakamakon fargabar kai harin ta'addanci a birnin.

Haɗin Kai Tsakanin 'yan Sanda, 'yan ƙasa Zai Inganta Zaman Lafiya - Masu Ruwa Da Tsaki.

Wasu masu ruwa da tsaki a harkar kare hakkin bil’adama a jihar Bauchi, a ranar Alhamis, sun bayyana cewa hadin kai da amana tsakanin ‘yan sandan Najeriya da ‘yan kasa zai inganta zaman lafiya a Najeriya.

'Ku Fice Daga Najeriya':Sakon Shugaban Amurica GA 'yan Kasar.

Gwamnatin kasar Amurka ta amincewa 'yan kasar mazauna Najeriya da su fara fita daga kasar biyo bayan rahoton barazanar tsaro da hukumomin kasar suka samo, Channels Tv ta ruwaito.