Latest News

Hare-haren Rasha Sun Jefa Kashi 10 Na Ukraine A Halin Rashin Lantarki- Zelensky

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce kashi 10 cikin 100 na al’ummar kasar yanzu haka na rayuwa ba lantarki sakamakon hare-haren Rasha da suka yi illa ga turakun wutar lantarki.

Tagwayen Bama-bamai Da Suka Fashe A Cikin Wata Mota Da Aka Kai Kan Wani Gini Na Ma’aikatar Ilimin Kasar

Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana cewa, tagwayen bama-bamai da suka fashe a cikin wata mota da aka kai kan wani gini na ma’aikatar ilimin kasar, ya hallaka mutane a kalla 100 kana wasu sama da mutum 300 sun jikkata.

Tashin Hankalin Burkina Faso Ya Raba Mutane Da Gidajensu

Bayanai daga Togo na cewa hare-haren ta’addanci a makwafciyar kasar Burkina Faso ya yi sanadin raba mutane fiye da dubu 4 da muhallan su. Jamhuriyar Benin da Ghana da kuma Ivory Coast na fuskantar baranazar fantsamar hare-haren ta’addanci.

Moussa Faki Mahamat Ya Bukaci A Dagewa Zimbabwe Takunkumai

Cikin wata sanarwa da aka fitar ga manema labarai da yammacin ranar Laraba, Mahamat ya ce yana sake jaddada kiraye-kirayen da AU ta jima tana yi, na gaggauta dagewa hukumomi, da wasu daidaikun ’yan kasar Zimbabwe takunkuman kasashen yamma ba tare da wasu sharudda ba.

Paparoma Francis Ya Gargadi Limaman Coci Game Da Kallan Batsa

"Kowane ɗayanku yana tunanin idan kun sami gogewa ko kuma kuna da jarabar batsa na dijital. Laifi ne da mutane da yawa suke da shi, ƴan ƙasa da yawa, mata da yawa har ma da limamai da mataimakansu, ”in ji Francis.

Syria Ta Bayar Da Rahoton Cewa Isra'ila Ta Kai Hari Ta Sama A Kan Wasu Wurare A Damascus

Kafofin yada labaran kasar Syria sun rawaito cewa, an kai hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a kusa da Damascus babban birnin kasar Syria, lamarin da ya kasance karo na uku cikin mako guda.

Yayin Da Yakin Ukraine Ke Jan Hankali Zuwa Wata Na Tara, Bala'in Rasha Ya Kara Tsananta

Yunkurin da sojojin Rasha suka yi na sake kai farmakin a birnin Kharkiv, inda a baya-bayan nan suka yi asarar fiye da murabba'in kilomita 8,000 (kilomita 3,088), bai yi tasiri ba. Sojojin Ukraine sun ce yanzu haka sun sake kwato matsugunai 544 a yankin, yayin da 32 kacal suka rage a mamaya.