Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron kolin kasar Sin da kungiyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa dake yankin Gulf karo na farko a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar 9 ga wata, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi. Wannan ne dai karo na farko da shugabannin kasar Sin, da shugabannin kasashen mambobin kungiyar suka gana kai tsaye, domin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakaninsu.
Rahotanni sun ce, shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce zai matsawa kasashen Japan da Holland lamba, don bukatar su hana fasahohin zamani na kera bangarorin hada na’urorin laturoni su shiga kasar Sin.
A yayin ganawar, Cui Jianchun ya bayyana cewa, babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, wani muhimmin lamari ne a tarihin harkokin siyasar jam'iyyar da jama'ar kasar Sin.