Dr Vincent Isegbe, babban darkta a hukumar kula da dabbobi da tsirrai a Najeriya (NAQS), shi ne ya saka hannu a madadin Najeriya inda Dr Javier Arriaga ya wakilci Mexico a birnin Mexico City.
FASA KORI:“Marigayin, mataimakin Sufeto, Saheed Aweda, an binne shi kamar yadda hakkin addinin Musulunci ya tanada a mahaifarsa, Popogbona a karamar hukumar Ilorin ta yamma a jihar Kwara.
Satar Man Fetur: Sojojin Ruwa Sun Mika Jiragen Ruwa masu anfani da Makamashi , Ma’aikata Ga EFCC A ranar Talata, 18 ga Oktoba, 2022 aka mika jiragen ruwa guda biyu, MT Platform da MV Caribbean Crest tare da wasu ma’aikatanta 22 da ake zargin barayin mai ne ga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati,
Za'a yi Jana'izar shi da misalin ƙarfe Biyu na Rana 2.00pm) Yau Litinin idan Allah ya kaimu lafiya, a garin Rimaye ƙaramar hukumar Kankia ta jihar Katsina.
Farhan Haq, mai magana da yawun babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, dakarun dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu, sun nuna damuwa matuka game da fadan da ake gwabzawa tsakanin matasan kabilar Dimka biyu masu dauke da makamai a arewacin kasar.
Tsohon kocin Super Falcons Godwin Izilein ya ce masu horar da ‘yan wasa na kasashen waje suna Najeriya ne kawai domin samun kudaden ritaya. Izilein ya kara da cewa Jose Peseiro ba shi da wani abin da zai iya bayarwa a Super Eagles.
Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Baba-Alkali, ya bukaci jami’an da aka tura cibiyoyin horas da ‘yan sanda da kada su dauki guraben da aka kaisu a matsayin hukuntawa.