Latest News

Rahotanni Sun Ce, Shugaban Amurka, Joe Biden, Ya Ce Zai Matsawa Kasashen Japan Da Holland Lamba

Rahotanni sun ce, shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce zai matsawa kasashen Japan da Holland lamba, don bukatar su hana fasahohin zamani na kera bangarorin hada na’urorin laturoni su shiga kasar Sin.

NAJERIYA DA MEXICO SUN KULLA YARJEJENIYAR KASUWANCIN ZOBO

Dr Vincent Isegbe, babban darkta a hukumar kula da dabbobi da tsirrai a Najeriya (NAQS), shi ne ya saka hannu a madadin Najeriya inda Dr Javier Arriaga ya wakilci Mexico a birnin Mexico City.

Hare-haren Rasha Sun Jefa Kashi 10 Na Ukraine A Halin Rashin Lantarki- Zelensky

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce kashi 10 cikin 100 na al’ummar kasar yanzu haka na rayuwa ba lantarki sakamakon hare-haren Rasha da suka yi illa ga turakun wutar lantarki.

Turkiya Za Ta Aiko Da Jiragen Sama Masu Saukar Ungulu Zuwa Najeriya

Jakadan Turkiya a Najeriya Hidayet Bayraktar ya ce nan ba da dadewa ba jiragen yaki marasa matuka da jirage masu saukar ungulu daga Turkiyya za su isa Najeriya.

Shugaban Nijer Mohammed Bazoum Ya Jagoranci Bikin Rantsar Da Shugaban Kotun Daukaka Kara Na Farko,

Shugaban Nijer Mohammed Bazoum ya jagoranci bikin rantsar da shugaban Kotun daukaka kara na farko, a kasar Abdou Galadima, da na shugaban majalisar jaha na farko, Mista Nouhou Hamani Mounkaila. An gudanar da bikin ne a cibiyar taron kasa da kasa ta Mahatma Gandhi da ke birnin Niamey.

Jirgin Shugaba Buhari Ya Tashia, Ya Nufi Kasar Koriya Ta Kudu

Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga tashar jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja inda ya nufi birnin Seoul, kasar Afrika ta kudu. Jirgin ya tashi ne da safiyar Lahadi, 23 ga watan Oktoba 2022.

A Jiya Juma’a Ne Aka Rantsar Da Kaftin Ibrahim Traore, A Matsayin Shugaban Kasar Burkina Faso Na Rikon Kwarya

A jiya Juma’a ne aka rantsar da Kaftin Ibrahim Traore, a matsayin shugaban kasar Burkina Faso na rikon kwarya, a gaban ‘yan majalissar kundin mulkin kasar a birnin Ouagadougou fadar mulkin kasar.