Latest News

Rahotanni Sun Ce, Shugaban Amurka, Joe Biden, Ya Ce Zai Matsawa Kasashen Japan Da Holland Lamba

Rahotanni sun ce, shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce zai matsawa kasashen Japan da Holland lamba, don bukatar su hana fasahohin zamani na kera bangarorin hada na’urorin laturoni su shiga kasar Sin.

Za A Gudanar Da Taron Baje Kolin Sararin Samaniya Na Kasa Da Kasa Karo Na 14

Za a gudanar da taron baje kolin sararin samaniya na kasa da kasa karo na 14 a birnin Zhuhai da ke gabashin kasar Sin daga ranar 8 zuwa 13 ga wata. Kwanan baya, manyan jiragen sama masu dakon kaya kirar Y-20 guda 2 sun taimaka wajen yin jigilar kayayyaki zuwa wajen taron. (Tasallah Yuan)

'Yan Bindiga Sun Sace Dattijuya 'yar Shekara 67 Da ɗanta A Katsina

Sharhi ta samu labari daga majiya mai tushe cewa, wasu ‘yan bindiga da ba a tantance yawansu ba, sun kai hari a garin Ingawa ta jihar Katsina, inda suka sace wata dattijuwa mai suna Gwaggo ‘Yar Ladi Turaki, wadda take da kimanin shekaru 67 a duniya.

Hare-haren Da Wasu ‘yan Bindiga Sama Da 200 Suka Kai A Kauyukan Da Ke Kusa Da Garin Kwari A Unguwar Bakalori Kwari,

Jami’an tsaro tare da hadin guiwar ‘yan sa-kai da sun dakile munanan hare-haren da wasu ‘yan bindiga sama da 200 suka kai a kauyukan da ke kusa da Garin Kwari a unguwar Bakalori Kwari, a karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Ya Halarci Tarurrukan Karawa Juna Sani, Tarukan Karawa Juna Sani, Da Taruka A Ciki Da Wajen Najeriya.

A halin yanzu yana rike da mukamai da dama masu tasiri a kungiyoyi masu zaman kansu da masu zaman kansu a ciki da wajen Katsina da ma Najeriya baki daya.

Sarkin Katsina Zai Dawo Gida Bayan Shafe Watanni Yana Jinya A Kasar Ingila

Mai Martaba Sarkin Katsina Na Dab Da Dawo Wa Gida Najeriya Bayan Duba Lafiyar Shi A Kasar Waje Majalisar Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman Ta Fitar Da Sanarwar Cewar Sarkin Katsina Zai Dawo Gida Najeriya A Ranar Lahadi Mai Zuwa 30 Ga Watan Oktoba, 2022 Daga Kasar Burtaniya Da Ya Je Domin Duba Lafiyarsa.

Baturiyar Data Shafe Shekaru 40 Tana Koyarwa Ta Rasu A Katsina

Innalillah ma'inna ilaihi raji'un mun samu labarin rasuwar Malama Amina Rivera da aka fi sani da y'ar Baturiya, dake GCK. Madam Amina wadda yar asalin ƙasar Phillphines ce, tazo Nijeriya tun shekaru 40 da suka gabata, inda ta sadaukar da dukkanin lokuttanta wajen koyarwa