Latest News

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping, Ya Halarci Taron Kolin Kasar Sin Da Kungiyar Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashen Larabawa Dake Yankin Gulf

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron kolin kasar Sin da kungiyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa dake yankin Gulf karo na farko a birnin Riyadh, fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar 9 ga wata, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi. Wannan ne dai karo na farko da shugabannin kasar Sin, da shugabannin kasashen mambobin kungiyar suka gana kai tsaye, domin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Sojoji Sunkashe 'yanta'adda 45 Sunceto Wadanda Akayi Garkuwa Dasu 45 A àrewa Tatsakiya

Rundunar sojin sama da ƙasa dake aiki a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya sun kashe mahara sama da 45 a cikin makonni biyu da suka gabata. Darektan yada labarai na hukumar manjo-janar Bernard Onyeuko ya sanar da haka da yake bayani kan nasarar da sojoji suka samu akan ƴan ta’adda. Onyeuko ya ce a Arewa ta Tsakiya rundunar sojin sama dake aiki karkashin ‘Operation Whirl Punch’ sun kashe gogarman ƴan bindiga Alhaji Shanono a kauyen Ukambo dake jihar Kaduna.