Labarai

An Yanke Wa Malamin Makaranta ɗaurin Shekara 15 Saboda Yi Wa ɗalibarsa Fyaɗe

Wata babbar kotu a jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya ta yanke wa wani malamin makaranta hukuncin ɗaurin shekara 15 saboda samunsa da laifin yi wa wata ƙaramar yarinya mai shekara takwas fyaɗe.

Ana zargin malamin makarantar da aikata laifin a shekarar 1999 a gidan su yarinyar.

A watan Agustan 2023 aka gurfanar da Oluwagbemi Alabi, mai shekara 45 a gaban kotun.

A lokacin da yarinya ta bayyana agabn kotu, ta ce malamin, wanda makwabcinsu ne kan riƙa tattaɓa jikinta a duk lokacin da ya je gidansu domin koya mata karatu.

”A lokacin ba na gane abin da yake nufi, har sai da wata rana ya haike mini, a falon gidanmu lokacin mahaifiyata ta yi tafiya zuwa Legas, ta bar ni a gida tare da ‘yan uwana”, in ji wadda aka yi wa fyaɗe – wadda a yanzu matashiya ce.

Kotu Yi Umarnin A Like Sammaci A Kofar Gidan Sadiya Icen-Kabari Bisa Zargin Bata SunaGwamnati ta gargaɗi ‘yan Najeriya kan shan gishiri fiye da ƙima

Ta ci gaba da faɗa wa kotun cewa Alabi ya cire tufafinta bayan kammala aika-aikar, inda ya yi amfani da shi wajen goge jinin da ya zuba a jikinta, sannan ya jefar da shi.

”Daga nan ne na ruga da gudu zuwa makwabtanmu ina kuka, sun ɗauka tafiyar mahaifiyarmu ce ta sa ni kukan, amma ban gaya musu abin da ya faru ba.”

Ta ce daga nan ba ta sake zuwa makaranta ba, saboda ba za ta iya mayar da hankali kan karatun ba, ”domin kuwa a duk lokacin da na gan shi a aji tsoro ne yake kamani”.

Ta ce ta sake haɗuwa da shi a shekarar 2012 a shafin Facebook, lokacin da ya aike mata da saƙon neman zama abokinta a shafin, amma sai ta ƙi amincewa da shi.

“A shekarar 2023, sai ya ci gaba da damuna, inda ya ci gaba da turo min saƙonni da bidiyoyi na rashin daraja, yana tuna min mummunan lamarin da ya faru a baya tsakaninmu, wanda kuma ba zan iya jurewa ba, daga nan sai na ɗauki matakin shari’a a kansa,” in ji ta.

A yayin da kotun ta nemi jin bahasin wanda ake zargin, ya amince da laifin da ake tuhumarsa da shi ba tare da wata fargaba ba.

Daga nan ne kuma alƙalin kotun, Mai shari’a Lekan Ogunmoye ya ce laifin da Alabi ya aikata na yin amfani da ƙarfi wajen haike wa ƙaramar yarinya babban laifi ne.

Daga nan ne kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 15 domin ya girbi abin da ya shuka.