Kwamitin malaman addinin musulunci na Najeriya ya goyi bayan auren marayu 100 da kakakin majalisar dokokin jihar Neja ya ƙuduri aniyar ɗaukar nauyi.
Cikin wata takarda da kwamitin ya fitar, mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin, Malam Aminu Inuwa Muhammad da sakatarensa, Engr Basheer Adamu Aliyu, sun ce abin da kakakin majalisar ke shirin yi abin a yaba ne, ba na kushewa ba.
Kwamitin ya ce duba da matsalar tsaro da matsin tattalin arziki da wasu yankunan arewacin Najeriya ke fuskanta, ɗaukar nauyin aure wani nau’i ne na tallafa wa marasa ƙarfi
”A shekarun baya-bayan nan jihar Neja da wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya na fama da matsalar tsaro da ‘yan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa, lamarin da ya shafi rayuwar mutanen yankin, iyalai da dama sun rasa iyayensu, kan haka ne shugabannin al’ummar yankin ke ƙoƙarin magance musu wahalhalun da suke fuskanta ta ɓangarori daban-daban, kamar yadda kakakin majalisar dokokin Neja ya yi yunƙurin yi”, in ji sanarwar.
Gwamnati Da NLC Za Su Sake Zama Kan Mafi Karancin Albashi.
NJC Ta Aikawa Alkalai 3 Da Takardar Gargadi Tare Da Hana Ciyar Dasu Gaba
”A matsayinmu na musulmi muna ƙoƙarin yin abubuwa kamar yadda shari’a ta tanadar, su kansu ‘yan matan sun zaɓi su yi aure, a maimakon su faɗa karuwanci ko a yi safararsu zuwa Turai kamar yadda wasu da ba su da hali ke yi don rage wa kansu matsin rayuwa”, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.
Kwamitin malaman addinin musuluncin ya ce abin da ministar ta yi bai dace ba.
”Abin da minista ta yi nuna wariya ne da wargaza abu mai kyau da rashin ƙwarewar aiki da kuma ƙabilanci, domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince da ‘yancin addinin tare da amincewa ta shari’ar musulunci da ta amince da aure”, in ji sanarwar.
A makon da ya gabata ne dai ministar mata ta Najeriya ta kai ƙarar kakakin majalisar dokokin jihar Nejan zuwa ga babban sifeton ‘yan sandan ƙasar bisa zarginsa da tilasta aurar da ‘yan matan da ta ce masu ƙananan shekaru ne.
Ministar ta ce idan taimakon ‘yan matan kakakin majalisar ke son yi, me zai hana ya ɗauki nauyin karatunsu, ko ya basu jari domin su tsaya da ƙafafunsu, a maimakon yi musu aure.
To sai dai ɗan majalisar ya kare matakin da cewa taimakon yaran ya yi, yana mai cewa galibinsu marayu ne waɗansa suka rasa iyayensu sakamakon matsalar tsaro da wasu sassan jihar ke fuskanta.