Labarai

Kotu Ta Bayar Da Umarnin ƙwace Kuɗi Da Wasu Kadarori Mallakin Emefiele

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a birnin Legas ta bayar da umarnin ƙwace kuɗi samada naira miliyan 800 da kuma wasu kadarori wadanda ke da jiɓi da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Mai shari’a Yellim Bogoro ne ta bayar da umarnin a ranar Alhamis, bayan buƙatar da lauyar hukumar EFCC, Bilkisu Buhari ta shigar.

Bayan sauraron ƙorafin da EFCC ta shigar, mai shari’a Bogoro ta ce: “Na saurari bayanin da mai shigar da ƙorafi ta yi kuma na amince.

An ƙaddamar sabon a-daidaita-sahu na mata zalla a KanoAn ƙaddamar sabon a-daidaita-sahu na mata zalla a Kano

“Akwai ƙwararan hujjo game da buƙatar da ta gabatar, saboda haka na amince da buƙatar.

Kuɗin da kotun ta umarci EFCC ta ƙwace sun kai dalar Amurka 4,719,054.