Mun fuskanci irin wannan matsalolin a Najeriya, amma ba mu yi ƙorafi ba - Libya
Hukumar kwallon Kafa ta Libya (LFF) tayi tsokaci kan matsalolin da Super Eagles ta Najeriya ke fuskanta a kasarta a halin yanzu.
Dimokuradiyya TV ta ruwaito yadda Tawagar ta Najeriya suka makale a filin jirgin ƙasar tsawon sa’o’i 14.
Bayan da Najeriya ta lallasa kasar Libya a ranar Juma'a a Uyo Jihar Akwa Ibom, za a fafata wasan zagaye na biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin AFCON 2025 a Benghazi ƙasar Libya ranar Talata.
Gabanin wasan zagaye na biyun, tawagar Najeriya ta ɗauki hanyar Benghazi ta hanyar jirgin sama a ranar Lahadi.
Sai dai kuma an karkatar da jirgin daga inda za su sauka sa'a guda kafin saukar su.
Ƴan wasan Najeriya sun sauka a filin jirgin sama na Al Abrak wanda kawai ake amfani da shi wajen gudanar da aikin hajji.
Bayan saukar su, hukumar ta NFF ta shirya tafiyar su ta cikin Mota zuwa wurin da za a yi wasan sakamakon rashin halartar jami’an hukumar kwallon kafar Libya.
Sai dai jami'ai a filin jirgin ba su bari motar bas ɗin da aka kawo musu ta shiga filin jirgin ba.
Bayan faruwar lamarin Super Eagles sun yanke shawarar ba za su buga wasan ba sai dai su koma gida.
Sai dai da ta ke yin tsokaci a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, hukumar kwallon kafa ta Libya LFF ta ce ba daidai ba ne a ce da gangan suka yi yunkurin musgunawa ga tawagar ta Najeriya duk da sun fuskanci kwatankwacin haka.
Mun damu matuka game da rahotannin baya-bayan nan game da karkatar da jirgin ƴan wasan Najeriya gabanin wasan neman shiga gasar cin kofin Afrika a Libya.”
Yayin da muke yin nadama game da duk wani rashin jin daɗi da suka fuskanta, yana da mahimmanci a lura cewa irin waɗannan abubuwan na iya faruwa saboda ka'idojin kula da zirga-zirgar jiragen sama na yau da kullun ko kuma ƙalubalen kayan aiki waɗanda ka iya shafar tafiye-tafiyen jirgin sama na ƙasa da ƙasa.